Hukumar EFCC ta tsare tsohon babban lauyan ƙasa Abubakar Malami bayan gazawarsa wajen cika sharudɗan belin da aka ba shi, lamarin da yasa aka ci gaba da riƙe shi har zuwa daren Talata.
Wata majiya daga hukumar ya tabbatar cewa Malami na nan a tsare saboda bai cika sharudɗan belin da aka gindaya masa ba, tare da cewa an bukaci tsohon ministan ya bayyana gaskiya game da zargin wasu kuɗaɗe da kuma bude asusun bayan-fage.
Rahotanni sun nuna cewa hukumar tana zargin Malami da hannu a daukar nauyin ta’addanci da kuma batun inda kuɗin Abacha na Dala Miliyan 346.2 da aka dawo da su daga Switzerland da kuma kudaden da suka fito daga tsibirin Jersey suka kare.
Hukumar ta ce zai kasance a tsare har sai ya cika sharudɗan da ake bukata.
Karanta: Tsohon Lauyan Gwamnatin Tarayya Malami ya musanta zargin tallafawa ayyukan ta’addanci
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa EFCC ta ce an ba shi belin farko amma bai cika sharudɗan ba, kuma ana tuhumarsa da laifuka da dama da suka hada da wanke kuɗi da cin zarafin ofis da daukar nauyin ta’addanci, inda hukumar ta ce tana gano karin bayanai a yayin bincike.
Wani bangare na rahoton ya nuna cewa hukumar ta bukaci Malami ya rika bayyana gaban masu bincike kullum har zuwa karshen watan Disamba, yayin da ake cigaba da gudanar da bincike kan laifuka kusan 18 da ake zargin yana da alaka da su.
A nasa bangaren, Malami ya musanta zarge-zargen, yana mai cewa ba su da tushe, tare da bayyana cewa a lokacin da yake mukami ya yi aiki tare da sauran hukumomi wajen karfafa tsarin dakile laifukan kuɗi da daukar nauyin ta’addanci a ƙasar.












































