Gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara ya sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulki a hukumance.
A daren Talata ya bayyana cewa ya yanke wannan shawara ne sakamakon goyon bayan da jihar ta samu daga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, wanda ya ce ya dace ya mayar da martani da irin wannan goyon baya.
Sauyin jam’iyyar ya kawo ƙarshen watanni na hasashen ko Fubara zai koma APC, lamarin da dama suka danganta da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma tsakaninsa da shugaban ƙasar.
Ana ci gaba da danganta sauya sheƙar gwamnan da yunƙurin tabbatar da zaman lafiya a siyasar Rivers, tare da ƙarfafa dangantaka da gwamnatin tarayya.
A halin da ake ciki, masu lura da al’amuran siyasa na ganin wannan mataki na iya sauya yanayin karfi da tasiri a jam’iyyun siyasar jihar Rivers a zaben da ke tafe.
Jam’iyyar APC ta tarbi Fubara tare da jiran cikakken bayani kan irin rawar da zai taka a sabon matsayinsa, yayin da magoya bayansa ke ganin tafiyar za ta ƙarfafa ci gaban jihar.
A gefe guda kuma, ana jiran martanin manyan jiga-jigan PDP dangane da ficewar gwamnan daga jam’iyyar.












































