Jami’an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC) sun kama wasu mutane uku da ake zargi da sayen ƙuri’u a wurare daban-daban na jihar Anambra yayin zaɓen gwamnan da aka gudanar a ranar Asabar.
Mai magana da yawun hukumar, Dele Oyewale, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.
Ya ce an kama mutanen ne sakamakon bayanan asiri da kuma sa ido da jami’an hukumar suka gudanar domin hana aikata maguɗin zaɓe.
Ya bayyana cewa an kama waɗanda ake zargi ne yayin da suke ba wa masu zaɓe kuɗi ko karɓar kuɗi daga hannun su domin sayen ƙuri’a.
Kuma an kama su ne a rumfar zaɓe ta biyu da ke ƙaramar hukumar Njikoka, da rumfar zaɓe ta biyu (008) da ke Awkuzu, ƙaramar hukumar Oyi, da kuma a ƙauyen Umunachi na ƙaramar hukumar Dukonukofia.
Hukumar ta ce waɗanda aka kama suna cikin aikin zaɓen gwamna da aka gudanar a ranar Asabar.
EFCC ta bayyana cewa za a gurfanar da su a kotu da zarar an kammala bincike a kansu.
NAN












































