Ƙaramin Ministan ayyuka, Bello Goronyo, ya bayyana damuwa kan yadda ake aikata munanan ayyuka na lalata aikin gina hanyar Abuja–Kaduna zuwa Kano.
Goronyo ya bayyana hakan ne yayin da yake duba aikin a ranar Asabar, inda ya bukaci shugabannin al’umma su ja hankalin mazauna yankunan da su guji irin waɗannan halaye marasa kyau.
Ya ce kamfanin da ke aikin yana aiki tukuru a wurin kuma aikin yana tafiya da kyau sosai.
Haka kuma, ya yi nuni da cewa kula da hanya da hana lalata kayayyakin da ke cikinta yana daga cikin muhimman matakan gyaran hanya.
Ministan ya bayyana cewa wasu mutane suna zuwa da dare suna karya sassan gada ko hanyoyi domin cire sandunan ƙarfe, musamman a gadar Jaji da ke Kaduna.
Haka kuma, wasu suna shimfiɗa hatsi, jefa shara ko kuma tono hanyar don saka wayoyi, lamarin da ke jawo lalacewarta.
Goronyo ya yi Allah-wadai da wannan dabi’a, inda ya roƙi shugabannin al’umma da ke bakin hanyar da su kula da mutanensu don tabbatar da cewa hanyar ta zauna lafiya.
Ya ce gwamnati ta kashe kuɗi da yawa wajen gina wannan babbar hanya, don haka wajibi ne a kiyaye ta.
Ya ƙara da cewa muhimmancin hanyar da ake kula da ita sosai ba zai misaltu ba, domin tana rage haɗurra, tana sa tafiye-tafiye su kasance cikin aminci da sauri, kuma tana taimakawa wajen tabbatar da tsaro.
Ya kuma ce, tun da aka fara aikin an rage matsalolin tsaro a yankin.
Haka kuma, ya bukaci matafiya da shugabannin al’umma su bayar da goyon baya ga gwamnatin Bola Tinubu wajen tabbatar da cewa hanyoyi sun kasance cikin koshin lafiya domin amfanin kowa da kowa.
A nasa ɓangaren, Daraktan manyan hanyoyi na ma’aikatar ayyuka ta tarayya, Clement Ogbuagu, ya bayyana cewa tawagar ta duba matakai daban-daban na aikin, kuma aikin yana tafiya cikin nasara.
Ya ce kamfanin da ke aikin yana yin aiki mai kyau, kuma suna ci gaba cikin sauri bisa jadawalin da aka tsara.
Ogbuagu ya bayyana cewa wannan hanya tana daga cikin ayyukan gina hanyoyi da suka fi tafiya cikin sauri a ƙasar nan a yanzu, kuma ingancin aikin yana da matuƙar gamsarwa.
NAN












































