Majalisar dokoki ta ƙasa ta takaita zirga-zirga a kusa da ofishin Akpabio saboda tsaro

Godswill Akpabio 750x430

Majalisar dokoki ta ƙasa ta sanar da sabbin matakan tsaro da suka haɗa da takaita zirga-zirga a kusa da ofishin shugaban majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata takarda mai ɗauke da kwanan watan 2 ga Oktoba, wadda babban jami’in tsaron Majalisar Etido Ekpo. sanya wa hannu.a

A cewar sanarwar, za a killace hanyar da ke haɗa zauren “White House” zuwa ofishin shugaban majalisar, domin amfani na musamman ga sanatoci da kuma ’yan majalisar wakilai kawai.

Sanarwar ta ce daga yanzu ba za a sake bari manyan sakatariyar sanatoci ko mataimaka na musamman su bi wannan hanya ba, domin tabbatar da tsaro da aminci a wajen gudanar da ayyukan majalisa.

Majalisar dokoki ta ƙasa za ta koma zaman majalisa a ranar 7 ga Oktoba bayan hutun fiye da watanni biyu.

NAN

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here