Shugaban Hukumar Zabe ta Bauchi Ya rasu

Alhaji Ahmed Makama Hardawa

Shugaban Hukumar Zabe ta Bauchi Ya ras
Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Bauchi, BASIEC, Alhaji Ahmed Makama Hardawa, ya rasu.

Mukhtar Gidado, mai baiwa gwamna Bala Mohammed shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, ne ya tabbatar da rasuwarsa a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

A cewar sanarwar, Alhaji Hardawa ya rasu ne a ranar Talata, 29 ga watan Yuli, 2025, a Abuja bayan gajeruwar rashin lafiya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here