Rikicin APC a Gombe : Abokin Gwamna Yahaya ya bayyana sha’awar kujerar Goje

FFECC70C 5C9C 4E07 B683 FAE96FFCEF31
FFECC70C 5C9C 4E07 B683 FAE96FFCEF31

Wani aminin siyasar gwamnan jihar Gombe, Alhaji Abubakar Mu’azu Hassan, ya bayyana cewa yana son tsayawa takarar kujerar Sanatan Gombe ta tsakiya, wanda a halin yanzu Sanata Danjuma Goje ke kai.

Habu Mu’azu, kamar yadda aka fi sani da shi, ya kasance shugaban matasa a lokacin da Goje ya rike mukamin gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar PDP.

Daga baya ya zama babban abokin gwamna Yahaya bayan sun samu sabani da Goje.

A watan Janairu ne dai shugabannin jam’iyyar APC na kasa suka yi yunkurin sasanta Goje da Yahaya.

Gwamna Mai Mala Buni, shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC, ya yi wata ganawar sulhu da ‘yan biyun a gidan Sanata Abdullahi Adamu a Abuja, sai dai da alama baraka ba ta kare ba.

Da yake magana a ranar Lahadi a garin Kumo da ke karamar hukumar Akko ta jihar, Mu’azu ya ce yana cikin fafutukar ne domin kawo ci gaba mai kyau da kuma ci gaba daga inda tsaffin wakilan majalisar dattawan suka tsaya.

A wajen taron da aka gudanar a gidan Kumo na Usman Bello Kumo dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Akko kuma babban abokin hamayyar Goje, Muazu ya shaidawa dubban magoya bayansa cewa ya samu albarkar Gwamna Yahaya kafin ya shiga takara.

Ya yi kira ga Goje da Sanata Abdullahi Idris Umar, da su ba wa matasa dama su ma su ba da gudummawar kason su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here