‘Yan bindiga sun kona al’umma a Birnin Gwari, sun yi awon gaba da mazauna garin

bandits attacks
bandits attacks

Al’ummomi da dama ne a karamar hukumar Birnin-Gwari ta jihar Kaduna wasu ‘yan bindiga su yi awon gaba da su a garin Birnin-Gwari.

‘Yan ta’addan sun afkawa al’ummomi kauyukan Awaro, Unguwar Shehu, Rhema da wasu al’ummomi a Dagara (da ke daura da dajin Kamuku) daga ranar Lahadi zuwa safiyar ranar Litinin, inda suka kona kauyuka tare da yin awon gaba da mutane tare da kwashe hatsi daga manoman.

An tabbatar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar tare da aika wa Solacebase a ranar Talata ta hannun kungiyar  Birnin Gwari Vanguard mai kula da harkokin tsaro da kyakkyawan shugabanci.

Sanarwar ta ce an kashe mutane uku a unguwar Sabon Gida, yayin da aka kashe mutum daya a unguwar Rhema da ke hakar ma’adinai da kuma sace mata uku da wasu maza da ba a tantance adadinsu ba, kuma an yi garkuwa da su cikin daji a wani sabon lamari da ya faru a Birnin-Gwari.

‘’An ga mata da yara da kuma tsoffi tun daga yammacin ranar Litinin har zuwa dare suna taruwa zuwa Birnin-Gwari a matsayin ‘yan gudun hijirar cikin gida. Al’ummomin Kungin DanBauchi da ke kan hanyar Birnin-Gwari- Funtua suma suna cikin garin Birnin-Gwari a matsayin ‘yan gudun hijira bayan da ‘yan bindiga suka kai hari ranar Lahadi,’’ inji sanarwar.

‘’Al’ummomin sun kaurace wa matsugunan su ne sa’o’i arba’in da takwas bayan da wasu ‘yan bindiga dauke da muggan makamai suka yi arangama da wani kasurgumin mai fada a Damari lamarin da ya sa akasarin al’ummar yankin tserewa zuwa Dogon-Dawa a matsayin ‘yan gudun hijira.

‘’Yanzu haka ‘yan bindiga sun kori kauyukan Kimbi, Katakaki da ke unguwar Kakangi a cikin dajin Birnin-Gwari mai makwabtaka da dajin Kuyanbana a jihar Zamfarsa, yayin da manoma suka kasa girbe amfanin gonakinsu, sakamakon hare-haren ‘yan bindiga da sace-sacen ‘yan fashi da makami.

Har yanzu dai ‘yan sanda da gwamnatin jihar ba su ce uffan ba kan hare-haren.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here