Za a gudanar da babban taron jam’iyyar APC a watan Fabrairu – Gwamnoni

APC Governors
APC Governors

Kungiyar Gwamnonin ta Progressives Forum (PGF), wato gwamnonin da aka zaba a jam’iyyar APC, ta ba da tabbacin cewa za a gudanar da babban taron jam’iyyar na kasa a watan Fabrairu.

Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi, wanda shine shugaban kungiyar ya bada wannan tabbacin a lokacin da yake zantawa da manema labarai a karshen wata ganawar sirri da suka yi a daren Lahadi a Abuja.

Bagudu, wanda bai bayyana takamaiman ranar da za a gudanar da taron ba, ya ce kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince, dole ne a gudanar da taron a watan Fabrairu.

Ya kara da cewa kwamitin riko da tsare-tsare na jam’iyyar APC shi yafi dacewa ya bayyana takamaiman ranar da za a gudanar da babban taron.

Bagudu ya ce taron ya amince da shugabancin kwamitin riko da tsare-tsare na jam’iyyar CECPC karkashin jagorancin Gwamna Buni da wasu gwamnoni biyu, Gwamna Muhammed Bello na Neja da Gwamna Gboyega Oyetola na Osun.

Ya kara da cewa gwamnonin sun yi wani gagarumin aiki na tafiyar da jam’iyyar cikin nasara tare da jan hankalin jama’a a cikin jam’iyyar, yana mai cewa kungiyar ta yi matukar farin ciki da halinsu.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa an sha matsin lamba ga shugabancin jam’iyyar karkashi Buni da ta tsayar da takamaiman ranar da za a gudanar da babban taron jam’iyyar bayan amincewar Buhari da a gudanar da taron a watan Fabrairu.

Wasu daga cikin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a ‘yan makonnin da suka gabata sun koka kan jinkirin da aka yi na bayyana wurin da kuma ainihin ranar da za a gudanar da babban taron.

Dr Salihu Lukman, Darakta-Janar na PGF, kwanan nan ya yi kira ga mambobin kwamitin riko na jam’iyyar da su yi murabus idan ba za su iya gudanar da babban taron jam’iyyar na kasa a watan Fabrairu ba.

Ana sa ran za a zabi sabbin mambobin kwamitin ayyuka na kasa (NWC) a babban taron.

Wadanda suka halarci taron sun hada da Gwamnonin Borno, Babagana Zulum, Jigawa, Mohammad Abubakar, Ondo State, Rotimi Akeredolu, Niger Abubakar Bello, Kaduna State, Nasir El-Rufai, Ekiti Kayode Fayemi, Kogi, Yahaya Bello.

Sauran sun hada da gwamnonin Cross River, Ogun, Zamfara, Ebonyi, Osun, jihar Legas, Imo, Plateau, jihar Kano da kuma Nasarawa.

Mataimakin gwamnan Anambra, Nkemakonam Okeke ne ya wakilci gwamnansa a taron.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here