Buhari ya yi alhinin rasuwar Bashir Tofa, ya aiko da wakilai domin yin ta’aziyya

D720A55E 7C8B 415B A62D 93A9F9D08C3D
D720A55E 7C8B 415B A62D 93A9F9D08C3D

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana Jimamin sa dangane da rasuwar Tsohon Dan takarar shugabancin Nigeria Marigayi Bashir Tofa, inda ya bayyana shi a matsayin mutum mai Dabbaka koyarwar addinin musulunci dana zamani.

Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata da ta fito daga fadar shugaban kasa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu.

Sanarwar tace Shugaba Buhari ya bayyana Marigayin a matsayin cikakken Dan ƙishin ƙasa wanda maye gurbin sa zai yi wuya.

A cewar Buhari” Bashir Tofa ya kasance Dan ƙishin ƙasa wanda ya taimaka wajen fito da dabarun  samar da ƙyaƙƙyawar Ƙasa da Shugabanci gare mu duka.”

Shugaba Buhari yayi addu’a Allah ya rahamshe shi ya kuma bada hakurin Juriya ga Iyali da Abokan sa, Masarautar Kano dama kuma Gwamnati da Al’umman jihar Kano bisa wannan rashi.

Haka nan kuma, Shugaban Ƙasa ya aike da Tawagar Wakilai zuwa Kano dauke da takardar Ta’aziyya ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano.

Tawagar sun kunshi Ministan Tsaro Manjo Janar Bashir Magashi Mai ritaya, da Ministan Albarkatun Ruwa Injiniya Sulaiman Adamu, da Babban Mai Tallafawa Shugaban kasa A Bangaren Yaɗa labarai Garba Shehu sai akanta janar na Gwamnatin Tarayya Ahmed Idris.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here