Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa EFCC ta hana ma’aikatan da ba’a yi wa allurar ragakacin Corona shiga ofishin hukumar.
Kamfanin dillacin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa tunda misalin karfe 7 na safiyar yau litinin aka fara tantance ma’aikatan hukumar, inda aka bawa wanda suke da shaidar yin allurar damar shiga, wanda basu da ita aka hana su.
Hukumar kula da yaduwar cutuka ta Nigeria NCDC ce sanar da tilastawa ma’aikata yin rigakafin biyo bayan bullar sabuwar kwayar cutar ta Corona mai suna Omicron a Nigeria.
Da yake jawabi ga manema labarai Sakataren hukumar ta EFCC Mr George Ekpungu ya ce ya zama dole su tabbata gaba daya ma’aikatan Hukumar sun yi rigakafin na Corona domin kaucewa yaduwar ta a tsakanin ma’aikatan hukumar.
Ya ce sun gudanar da wannan aiki ne bisa umarnin shugaban hukumar Abdulrasheed Bawa na tabbatar da cewa an bi sharudan da hukumar NCDC ta shimfida na kare kai daga cutar ta Corona.
Sakataren na Hukumar EFCC ya ce zasu duba matakin da zasu dauka kan ma’aikatan da suka ki yin rigakafin na Corona.










































