Tuni anyi Jina’izar Babban Limamin Masallacin Juma’a Na Fagge a Kano, Sheikh Nasir Muhammad Nasir

eef0eb569e2feaaa
eef0eb569e2feaaa

A yau Alhamis akayi jana’izar babban limamin masallacin Juma’a na Fagge, Sheikh Nasir Muhammad Nasir, a kofar Kudu dake fadar mai martaba sarkin Kano.

Babban malamin ya rasu ne a ranar Laraba 7 ga watan Yuni bayan ya yi fama da jinyar rashin lafiya.

Malamin addinin musuluncin wanda aka fi sani da Limamin Waje ya rasu yana da shekara 87 a duniya.

Marigayi sarkin Kano Ado Bayero, ya taɓa naɗa marigayin sarautar Wazirin Kano, amma tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya cire shi daga sarautar.

Kwankwaso ya maye gurbinsa ne saboda dalilan tsaro amma marigayin ya ƙi yarda ya sauka daga kan sarautar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here