Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa bai da tabbacin gwamnatin jam’iyyar da zai mikawa mulki a ranar 29 ga watan mayun shekarar damuke ciki ta 2023.
Ganduje ya bayyana haka ne yayin gangamin bikin bude titin Ahmadu Bello way dake nan kano.
”ina fatan gwamnatin da zata gaje ni ko ta NNPP ko ta APC Allah ne kadai ya sani, Amma dai Ina fata zasu karasa ayyukan da muka bari bamu karasa ba, kamar yadda muma muka yi”. Inji Ganduje
Gwamnan yace kowacce gwamnati ta kan tafi ta barwa ta bayan ta aiki, don haka ba sabon abu bane, kawai abun da ya ke fata shine kar Abar ayyukan da ya faro don gudun barnatar da kudaden al’umma jihar kano.
”Mun gudanar da ayyuka masu tarin yawa a wa’adin gwamnatin na, kuma dukkanin kananan da manyan ayyukan na yi Imani zasu taimaka wajen inganta kasuwanci da tattalin arzikin jihar kano da na kasa baki daya”.
Ganduje dai ya bude ayyukan titin da ya tashi daga Goron dutse zuwa kasuwar kurmi wato Sheikh Mahmoud Salga Road dake karamar hukumar Dala da titin Kwarin akuya dake karamar hukumar Fagge, sai kuma titin Gashash Road dake Nasarawa GRA da Kuma na Ahmadu Bello way.
Gwamna Ganduje a ‘yan kwanakinnan anjiyo shi ya na ta bankwana da mutane la’akari da gabatowar wa’adin mika mulki ga sabuwar gwamnati daza ta karbe ragamar gidan gwamnati na Africa House.













































