Fitaccen malamin addinin Islama a Najeriya da ke da’awar yi wa ƴan fashin daji masu satar mutane wa’azi, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi gargadin cewa za a yi da na-sanin ayyanasu a matsayin’ yan ta’adda.
Malamin ya faɗi haka ne cikin wata sanarwa da aka wallafa a wani shafinsa na Facebook.
Tuni dai ƴan majalisa suka nemi gwamnatin Tarayya ta ayyana ƴan fashin da suka addabi arewacin kasar a matsayin ƴan ta’adda.
A cikin sanarwar, Sheikh Gumi ya yi gargaɗin cewa “da zarar an ayyana ƴan fashin daji a matsayin ƴan ta’adda ƙungiyoyi masu da’awar jihadi na ƙasashen waje za su shiga lamarin dumu-dumj.
Ya kuma ce wannan zai iya janyo ra’ayin matasan da ke fama da rashin aikin yi.
A cewar Sheikh Gumi “Babu wanda ke shakkar cewa son raine a yau ya mamaye siyasarmu. Don ci gaba, dole ne wasu su fito su yi magana”.
Sai dai kuma a cikin bayanansa malamain ya bayyana cewa ayyukan da ƴan fashin daji ke aikatawa sannu a hankali sun zama na ta’addanci – “saboda duk inda ake kashe mutanen da ba su ji ba su gani ba, shima ta’addanci ne tsantsarsa.”













































