Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta bullo da sabon tsarin fasaha don sarrafa bayanan kowacce mota da mallakarta.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Olumuyiwa Adejobi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Abuja.
Adejobi ya bayyana cewa, an gabatar da tsarin ne a ci gaba da kaddamar da sashin yin rajistar (CMR) da kuma kaddamar da matakin farko na a shafin yanar gizo.
Ya bayyana cewa dole ne a yi rajistar bayanan abin hawa da CMR ya gabatar kimanin shekaru bakwai da suka gabata wanda zai magance kalubalen da ake fuskanta da akeyi wajan cikewa da hannu.
Ya kara da cewa CMRIS da aka yi amfani da shi zai yi aiki yadda ya kamata don samun ƙarin bayani daga jama’a game da motocin da aka sace da kuma cika bayanan motocin da aka sace.
“An sanar da masu motocin da jama’a cewa sabuwar hanyar neman sabis ta yan sanda shine CMRIS ta https://cmris.npf.gov.ng/
Irin waɗannan ayyuka sun haɗa da, Bayanan Motoci, Canjin Mallaka, Canjin Injin / Chassis / Jiki, Canjin Launi, Takaddun Motoci na Duniya da Izinin Direbobi na Duniya, da sauransu.
“Sufeto-Janar na ‘yan sanda (IG P) ya ba da umarnin dakatar da aiwatar da tsarin da rubutun hannu duk da bayar da takaddun shaida na CMR da ƙaura zuwa dandamalin NPF CMR na zamani.












































