Magatakardan Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) Farfesa Jamilu Ahmad Salim ya rasu.
A safiyar Laraba aka gudanar da jana’izarsa a masallacin Juma’a da ke sabuwar harabar jami’ar da ke titin zuwa Gwarzo.
Kafin rasuwarsa dai shi ne magatakardar BUK tun daga shekarar 2021, bayan maye gurbin Hajiya Fatima Bint Muhammad da ta shafe shekaru biyar kan matsayin.
An haife shi a ranar 21 ga watan Nuwamba a 1963 a unguwar Gwale da ke Kano, kuma ya kammala digirinsa na farko a Fannin Hausa/Islamic Studies a shekarar 1988.
Hakazalika ya yi aiki a bangarorin jamiar da dama kafin zamowarsa magatakardan jamiar a watan Oktoban 2021.
Da fatan Allah Ya ji kan sa, Ya kuma yi masa rahama. Amin.













































