2023: Inuwa Waya Yayi Ritaya Daga NNPC, Da Alamu Zai Yi Takarar Gwamnan Kano

inuwa ibrahim waya
inuwa ibrahim waya

Babban Manajan Rukunin da ke kula da Sufurin Jiragen Ruwa a Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC), Inuwa Waya, ya sanar da matakin yin murabus a ra’ayn kansa daga kamfanin a watan Disamba na wannan shekarar.

Kodayake har yanzu NNPC ba ta tabbatar da ritayar bababn ma’aikacin nata ba, amma wasu majiyoyi da yawa a NNPC da ke Abuja sun tabbatar da hakan a ranar Juma’a cewa Mista Waya ya riga ya mika wasikar tasa ta ajiye aikie a kashin kansa daga Kamfanin.

Daya daga cikin majiyoyin da suka nemi a sakaya sunansa, saboda bai cancanci yin magana kan lamarin ba, ya ce biyo bayan mika wasikar ritayar sa, Mista Waya ya riga ya fara aikin watanni uku kafin ritaya da ake yi, wanda ya fara a ranar 10 ga Satumba.

Majiyar ta ce Mista Waya da kansa ya ba da labarin yanke shawarar ritaya daga kamfanin mai na kasa a wani bukin zagayowar ranar haihuwa ta ba -zata da ma’aikatan sashen sufuri na kamfanin suka shirya don girmama ranar haihuwarsa ta cika shekara 58 a ranar Juma’a, 10 ga Satumba.

Karanta Wannan:Abdurrasheed Bawa Ya Murmure- EFCC

A cikin jawabin sa yayin bikin, majiyar ta ce Mista Waya ya sanar da ma’aikatan cewa bayan ya yi wa Kamfanin hidima sama da shekaru 30, lokaci ya yi da ya kamata ya dakata, ta hanyar yin murabus a kashin kansa don share fage ga masu tasowa su cigaba da jan ragamar.

Yawancin ma’aikatan sun ce sun yi mamakin sanarwar Mista Waya, ba tare da la’akari da cewa har yanzu yana da shekaru biyu a cikin aikinsa a NNPC na cika shekaru 60 na ritaya a hukumance.

Duk da cewa Mista Waya bai bayyana wasu dalilan sa ba amma wasu majiyoyi da ba a tabbatar da su ba na kusa da shi sun yi bayyana cewa yana nazarin takarar gwamnan jihar Kano a zaben 2023 mai zuwa.

SHARHI 1

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here