Buhari Ya Tafi Taron Majalisar Dinkin Duniya na 76 a Amurka

Buhari for UNGA
Buhari for UNGA

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar Abuja a wanna Lahadi zuwa New York don halartar taron Majalisar Dinkin Duniya na 76 (UNGA76).

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa zaman zai fara ne a ranar Talata, 14 ga watan Satumba.

Shugaban na Najeriya zai yi jawabi ga Majalisar a ranar Juma’a, 24 ga watan Satumba kan jigon taron da sauran batutuwan da suka shafi duniya.

Karanta Wannan: 2023: Inuwa Waya Yayi Ritaya Daga NNPC, Da Alamu Zai Yi Takarar Gwamnan Kano

Mista Adesina ya ce Shugaban zai yi jawabi ga Majalisar yayin jawabin bai daya a ranar Juma’a, 24 ga Satumba inda zai yi magana kan mauduín taron da sauran batutuwan da suka shafi halin duniya.

Ya kara da cewa Shugaban kasa da sauran mambobin za su halarci wasu muhimman tarurruka kamar taron tsarin abinci da babban taro na musamman don tunawa da ranar kasa da kasa ta kawar da makaman Nukiliya.

Ana kuma sa ran Shugaba Buhari zai gana da wasu shugabannin wasu wakilai da shugabannin kungiyoyin raya kasa da kasa yayin da yake a kasar Amurka.

Daga cikin wadanda za su yi masa akiya akwai Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama da Ministan Shari’a, Abubakar Malami, da Karamin Ministan Muhalli, Sharon Ikeazor.

A cewar hadimin shugaban kasa, ana sa ran shugaba Buhari zai dawo ranar Lahadi, 26 ga watan Satumba (NAN)

SHARHI 1

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here