Ƴan sanda sun tabbatar da mutuwar mutane 26, uku sun jikkata sakamakon harin da aka kai kan wasu al’umma a Jos

Police olopa sabo

Rundunar ‘yan sanda a Jihar Plateau ta bayyana cewa mutane 26 sun rasa rayukansu sakamakon harin da aka kai da daren Lahadi a Angwan Rukuba, wasu al’umma da ke karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Bassey Ewah, ne ya tabbatar da hakan a ranar Litinin a Jos, inda ya kuma ce mutane uku sun samu raunuka a harin.

Ya bayyana hakan ne yayin da gwamnan jihar, Caleb Mutfwang, ya kai ziyarar jaje ga iyalan wadanda abin ya shafa da kuma al’ummar yankin.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa wasu ‘yan bindiga sun kai harin ne da daren Lahadi cikin salo na musamman, inda suka kashe mutane da dama tare da jikkata wasu.

Kwamishinan ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, amma ya tabbatar wa jama’a cewa jami’an tsaro za su kamo wadanda suka aikata laifin.

Tun da fari, mai kula da yankin Arewa na kungiyar matasan Plateau, Ciroma Samson, ya ce harin ya faru ne da misalin karfe 7:30 na yamma a ranar Lahadi.

Ya tabbatar da adadin wadanda aka kashe da wadanda suka jikkata kamar yadda kwamishinan ‘yan sanda ya bayyana, amma ya bukaci gwamnati ta kara daukar matakai na gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyi.

Ya kara da cewa, bisa ga bayanan shaidu, ‘yan bindigar kimanin su 10 sun iso cikin wata motar Sharon, inda suka fara bude wuta kan mutanen da ke zaune ko tsaye a gefen hanya.

Samson ya kuma bukaci gwamnati ta taimaka wa iyalan wadanda suka mutu, yana mai cewa yawancin wadanda aka kashe su ne masu ciyar da iyalansu abinci.

saynnan ya kara da cewa bayan ziyarar gwamnan, an kai gawarwakin wadanda suka mutu dakin ajiye gawa bayan sun dauki lokaci a wurin da lamarin ya faru.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here