Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC ta ce, ta karbi wasiku daga kungiyoyi guda 110 da suke neman a yi mata rajista domin su koma matsayin jam’iyyun siyasa gabanin babban zaben shekarar 2027 da ke tafe.
Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya bayyana hakan yau Laraba a Abuja, yayin taron zartaswar da hukumar ke yi na kowane wata uku.
Ya ce, hukumar za ta bibiyi duk wasu bukatu cikin adalci ba tare da la’akari da matsayin masu tallata su ba.
A cewarsa, ya zuwa ranar Litinin hukumar ta samu wasiku daga kungiyoyi 110 da ke son yin rijistar jam’iyyun siyasar, Sai dai shugaban hukumar ta INEC, ya musanta rade-radin da wasu ke yi na cewa hukumar na tauye ‘yancinta kan matsayin kungiyoyin da ke neman yi musu rajistar.
Ya kuma yi tariyar baya inda ya bayyana cewa a shekarar 2013 an yi irin wannan zargi mara tushe da ke cewa hukumar ba ta da sha’awar hadewar jam’iyyun siyasa.
Yakubu ya bayyana cewa a yau Laraba hukumar za ta fitar da cikakken jerin sunayen kungiyoyi 110 da ke neman rajista da sunayensu da da adireshi da sunayen shugabanni da sakatarorinsu.
A yayin gudanar da zabukan fitar da gwani da kuma sake ci gaba da rijistar masu kada kuri’a CVR, ya ce a yanzu INEC na da damar gudanar da zaben da kuma ci gaba da yi wa mutane rijista a fadin Najeriya.
Da ya ke magana kan zaben kananan hukumomin babban birnin tarayya FCT mai zuwa, shugaban hukumar ta INEC, ya bayyana cewa za a kammala zaben fidda gwani na jam’iyyun siyasa a ranar 30 ga watan Yuni, inda ya kara da cewa an riga an samu bayanan tantance yanki a shafin hukumar.
Da ya ke magana kan zaben gwamnan Anambra da za a yi a ranar 8 ga watan Agusta, Yakubu ya ce, tuni aka fara yakin neman zabe a bainar jama’a da jam’iyyun siyasa suka fara yi tun a ranar 11 ga watan nan da muke ciki na Yuni kuma za a kammala ranar 6 ga watan Nuwamba.
Ya nanata cewa hukumar za ta ci gaba da sanar da jama’a game da harkokin zabe, inda ya bukaci kafafen yada labarai da su sanya ido kan harkokin zabe da na siyasa a babban birnin tarayya Abuja da Anambra.
A nasa jawabin, shugaban kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya NUJ, Alhassan Yahaya, ya yaba wa INEC kan yadda ake gudanar da harkokin yada labarai da kuma kokarin da hukumar ke yi na inganta zabe a Najeriya.
Ya kuma bai wa INEC tabbacin ci gaba da goyon bayan kafafen yada labarai yayin da ya yi kira ga hukumar da ta ba da fifiko kan tsaron lafiyar ‘yan jarida a zaben gwamna mai zuwa a Anambra.
NAN













































