Zargin Bata Suna: Kotun ta bayar da belin Sowore kan kudi Naira miliyan 200

sowore2 (1)

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Talata ta bayar da belin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, kan kudi Naira miliyan 200 da masu tsaya masa biyu.

A cikin hukuncin sa kan bukatar Sowore na dakatar da aiwatar da umarnin soke belin da aka bashi tun da fari, Mai Shari’a Mohammed Umar ya ba da umarnin cewa dole ne daya daga cikin masu tsaya masa ya zama sarkin gargajiya daga al’ummar Sowore.

Mai Shari’a Umar ya yanke hukunci cewa dole ne mai tsaya masan ya mallaki filin a Abuja.

Mai shari’ar, wanda ya ce dole ne masu kara su tabbatar da masu wadanda za su tsaya masan, ya kuma ba da umarnin Sowore ya mika fasfo din sa na tafiye-tafiye ga mataimakin babban mai rijista na kotun.

Mai shari’ar ya mika wanda ake kara ga lauyoyinsa sannan ya dage karar zuwa ranar 6 ga watan Yuli domin Sowore ya fara kare kan shi.

Tun da farko, Mai Shari’a Umar ya soke umarnin soke belin wanda ake kara da aka yi a karon farko da kuma umarnin a daure shi a gidan gyaran hali na Kuje.

Kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN), ya ruwaito cewa Mai Shari’a Umar a ranar 22 ga watan Yuni ya ba da umarnin a tsare Sowore, wanda shi ne editan Sahara Reporters, a gidan gyaran hali ta Kuje.

A wani kwarya-kwaryan hukunci da ya yanke, Mai shari’ar ya ba da umarnin a ajiye Sowore a gidan gyaran hali har sai an saurari bukatar da ya shigar kuma an yanke hukunci akanta na dakatar da umarnin soke beli da takardar kamu da Lauyansa Adeyinka Olumide-Fusika, (SAN) ya shigar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here