Zanga-zanga: Kotu ta tsare lauya da ɗan uwan Nnamdi Kanu tare da wasu 11 a gidan yari

Nnamdi Kanu Lawyer

Kotun majistare da ke Kuje, Abuja, ta tsare Yarima Emmanuel Kanu, ɗan’uwa ga jagoran haramtacciyar ƙungiyar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, wanda yake tsare sama da shekaru biyar a hannun gwamnatin tarayya.

Haka kuma kotu ta tsare lauyan Nnamdi Kanu, Aloy Ejimakor, a gidan yari.

An kama su ne yayin zanga-zangar #FreeNnamdiKanuNow da aka gudanar a ranar Litinin, 20 ga Oktoba.

An gurfanar da su tare da wasu mutum 11 a gaban kotu a ranar Talata, inda rundunar ‘yan sanda ta tuhume su da tada hargitsi da karya zaman lafiya a bainar jama’a.

Zanga-zangar ta jawo cunkoso a babban birnin tarayya Abuja, inda ma’aikata da direbobi suka kasa isa wuraren aikinsu.

‘Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zangar bisa hujjar cewa akwai umarnin kotu da ya hana su shiga wasu yankuna na birnin.

A makon da ya gabata, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta hana Omoyele Sowore da wasu gudanar da zanga-zanga a wasu wurare kamar fadar shugaban ƙasa, majalisar dokoki, hedkwatar ‘yan sanda, kotun daukaka ƙara, Dandalin Eagle da hanyar Shehu Shagari, har sai an kammala sauraron karar da aka shigar.

Alƙali Mohammed Umar ne ya amince da buƙatar gaggawa da lauya Wisdom Madaki ya gabatar wa kotu a madadin gwamnatin tarayya.

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa matakin na kotu yana da nufin tabbatar da zaman lafiya da gujewa rikici yayin da ake ci gaba da sauraron shari’ar Nnamdi Kanu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here