Zaben 2023: Sha’aban ya fita daga APC zuwa ADP, inda ya karbi tikitin takarar gwamna a jam’iyyar

Shaaban Ibrahim Sharada 1 1
Shaaban Ibrahim Sharada 1 1

Dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Municipal, Shaaban Ibrahim Sharada, ya fita daga APC zuwa jam’iyyar ADP.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta tattaro bayanan cewa dan majalisar ya sami tikitin takarar gwamna a jam’iyyar ta ADP bayan komawar sa.

Rahotan ni sun bayyana cewa sha’aban din zai yi takarar ne tare da Rabiu Bako, a matsayin wanda zai masa mataimaki.

Wani makunsancin Shaaban, wanda baya so a bayyana sunan sa ya tabbatarwa da Solacebase cewa dan majalisar zai bayyana fitar tasa dashi da magoya bayan sa kafin karshen wannan mako.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here