Gwamna Bello Matawalle, na Jihar ya sanya dokar hana hawa babur a Gusau babban birnin Jihar daga karfe 8 na daren ko wacce Rana zuwa 6 na safe.
Matawalle, ya Kuma umarci jami’an tsaro cewa duk wanda suka samu da laifin karya sabuwar dokar to su harbe shi.
A cewar gwamnan, matakin na zuwa ne bayan kwamitin tsaro na Jihar ya samu rahotannin cewa Yan bindiga da sauran masu aikata miyagun laifuka na amfani da baburan a cikin babban birnin Jihar da kewaye.
Ya ci gaba da cewa, “Idan aka yi la’akari da farmakin da ‘yan bindiga suka kai a wasu yankuna da ke wajen garin Gusau, babban birnin jihar, an haramta hawan babura daga karfe 8 na dare zuwa karfe 6 na safe a dukkan yankunan dake kewaye da garin Gusau.

“Yankunan da abin ya shafa sun hada da Mareri da Damba da Tsunami da Tsauni da Barakallahu da Samaru da Gada Biyu da Kuma Janyau Gabas”.
Matawalle ya jaddada cewa, tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma shi ne babban aikin kowace gwamnati.
“Gwamnatina tana yin duk mai yiwuwa bisa ga dokokin kasa don tabbatar da sauke wannan nauyi”.













































