Zaben 2023: Gwamna El-Rufai Ya Bayyana Abinda Ya Tayar Masa Da Hankali Lokacin Zabe 

06c9e227 nasir el rufai
06c9e227 nasir el rufai

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa yadda aka yi amfani da kuɗi wajen siyan ƙuri’u a babban zaɓen 2023, ya tayar masa da hankali. Gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Lahadi, 21 ga watan Mayun 2023, yayin zantawa da manema labarai a birnin tarayya Abuja.

“Na ga mutanen kirki da suka yi takara amma sun faɗi zaɓe. Sun sha kashi ne kawai saboda ana ba mai yin zaɓe N5,000 a ranar zaɓe.

“Ka yi tunani kaga dun wanda ya baka kuɗi ka zaɓe shi a lokacin zaɓe. Ka bashi makullan asusun dukiyar al’umma ne har na tsawon shekara huɗu ya je ya mayar da N5,000 ɗinsa.”

Tsohon ministan na birnin tarayya Abuja, ya bayyana cewa yawan siyan ƙuri’ar da aka yi ya janyo ƴan takarar da suka cancanta, ta kife da su. Ya yi nuni da cewa irin hakan ne ke sanyawa, ƴan siyasa su sace dukiyar al’umma.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here