Yan Sanda sun tabbatar da Sace Kwamishina a Jihar Nasarawa

Nigeria Kidnappings Bandits deputy
Nigeria Kidnappings Bandits deputy

Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta tabbatar da cewa Yan bindiga sun sace Yakubu Lawal, kwamishinan yada labarai, al’adu da yawon bude ido na jihar.

Mai magana da yawun rundunar a Jihar DSP Ramhan Nansel, shi ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata aka Kuma rabawa manema labarai a Lafia, babban birnin jihar.

“Da isar mu wurin, mun gano cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suna ta harbe-harbe, lokacin da Suka farmaki gidan kwamishinan yada labarai, al’adu da yawon bude ido suka yi awon gaba da shi.

Ya kara da cewa, “yanzu haka ana ci gaba da bincike da Kuma kokarin ceto Kwamishinan da sauran wanda lamarin ya shafa daga hannun Yan bindigar, karkashin jagorancin kwamandan yankin Akwanga, ACP Halliru Aliyu.”

Mai magana da yawun rundunar Yan Sandan ya ce Kwamishinan ‘yan sandan ya bayar da umarnin cewa duk wanda ke da bayanan da zasu taimaka wa hukumar wajen ceto wanda aka sace tare da kama masu garkuwa da mutanen kofa a bude take.

so
Kazalika ya Kara da cewa duk Wanda ke da wani bayani zai iya tuntubar rundunar ta lambobi kamar haka: 08035951018, 08033806409, 08037461715 da kuma 08036157659.

Kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN) ya tawaito cewa, a ranar Asabar din da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari tare da kashe ma’aikaciyar makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnatin Jihar Nassarawa-Eggon da ke karamar hukumar da aka yi garkuwa da Kwamishinan Yada Labaran.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here