Yan bindiga sun sako ragowar dalibai 3 na kwalejin gwamnatin tarayya ta Birnin Yauri, dake Kebbi da sukai garkuwa da su.
“Mun shafe kwana bakwai muna tattaunawa da yan bindaga a cikin daji kafin su yarda su sakar mana raguwar yaran mu.” Inji shugan kungyar iyayen daliban wadan da suke fafutikar samun yanci ‘ya ‘yan su.
Ragowar daliban da suka saki su ne Elizabeth Ogechi Nwafor, Esther Sunday da kuma Aliya Abubakar.
Shugaban kungiyar iyayen yaran Malam Salim Kaoje, ya shaidawa wakilin mu cewa raguwar daliban sun isa Kebbi ranar Litinin da yamma.
Sai dai kuma bai bayyana mana cew ko sun biya kudin fansa kafin a sakar musu yaran su ba.
An tattaro bayanai cewa jagoran yan ta’addan Dogo Gide, ya sako mata hudu a watan da ya gabata, wadan da ya saki sune Bilha Musa, Faiza Ahmed, Rahma Abdullahi da kuma Hafsa Murtala.
Ya bayyana cewa iyyen yaran sun biya kudin fansa kafin sakin yaran da Dogo Gide ya yi, yace sun sayar da kadarorun su da kuma tallafi da suka samu daga yan Najeriya kafin su biyan kudin fansar.
A watan Junairu Kaoje ya tabbatar da cewa sun tattauna da jagoran yan ta’addan, Dogo Gide sakamakon sa baki da mahaifiyar sa tayi.













































