Wike ya ce bai san lauyoyin da suka kai karar Atiku kotu da sunan sa ba

R L Atiku Abubakar and Nyesom Wike
R L Atiku Abubakar and Nyesom Wike

Gwamnan jiahar Revers, Mista Nyesom Wike, yau Juma’a ya nisanta kansa daga karar da aka ce ya kai Atiku, domin kotu ta cire Atiku daga matsayin dan takarar ta bawa Wike, a kakar zabe mai zuwa.

Hakan na zuwa ne sa’o’I kadan da rahoton da ya fita cewa gwamna Wike da shi da Newgent Ekamon sun shigar da karar mai FHC/ABJ/CS/782/2022, suna neman kotu ta kwace takarar Atiku ta bawa Wike.

Ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da jaridar THISDAY, a yau juma’a, Wike ya ce shi bai san wadan da suka shigar da karar ba.

“Ni ban sa kowa ya shigar da kara da sunanna ba”

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here