Babban Daraktan Hukumar Lafiya ta Duniya, Dakta Tedros Ghebreyesus ya bayyana kwarin gwiwa cewar akwai yiwuwar za a murkushe cutar Covid_19 ta hanyar kawo karshen ta a 2022
Awani taron manema labarai, Ghebreyesus yace shekaru biyun kenan dasuka shude cutar ta bayyana adaidai lokacin da mutane kê bikin murnar shigowar sabuwar shekara.
Tun a tsawon wannan lokacin, an Sami Rahoton mutuwar mutanen Kimanin Milyan 1.8 a shekarar 2020, yayin da rahoton ya nuna mutane Milyan 3.5 ne suka kwanta dama a 2021, yayin da rahoton yanuna milyoyin jamaa kê jinyar fama da cutar a tsawon lokacin.
Ayanzu haka dai, ana samun karin rahotannin yaduwar nau’ukan cutar corona samfurin Delta da Omicron, Wanda hakan kê kara adadin mutane marasa lafiya dake kwanciya a asibitoci.
“Gaskiya mun damu matuka da yadda nau’in corona samfurin Delta kê cigaba da kwarara tamkar wutar daji” Inji Ghebreyesus
A taron kasashe G7 da G20, masu karfin tattalin arziki da aka gudanar a 2020, WHO ta kalubalanci jagorori dasu tabbata sunyiwa al’ummar su rigakafin cutar da kaso 40 kafin kwarewar 2021, yayin dasuke saran kaiwa kusan kaso 70 a tsakkiyar 2022
Ghebreyesus daganan ya alakanta rashin samun tagomashi da ake samu akasashe masu karancin tattalin arziki atsawon shekaru, Inda ya bayyana damuwa kan yadda ake tura musu sinadaran alluran rigakafi da wa’adin su yazo karshe.
“Wannan shine lokacin da za a magance karancin rigakafin da ake samu awasu kasashe dan kare jamaa, tattalin arziki daga durkushewar sakamakon barazanar cutar” Inji Ghebreyesus
Tun da fari, Daraktan Hukumar yace kawo karshen cutar abune me sauki, idan kasashe suka hade kawunan su, domin hakan wani jigone na murkushe kowacce irin barazanar anan gaba.













































