Wakilan PDP sun fice daga ɗakin tattara sakamakon zaɓen Shugaban ƙasa da ke gudana a Abuja

c198ceda d97e 468a 9815 e0a871e9acd5
c198ceda d97e 468a 9815 e0a871e9acd5

Wakilan jam’iyyun PDP da na Labour Party sun fice daga ɗakin da ake tattara sakamakon zaben shugaban Kasa dake gudana a babban birnin Tarayya Abuja.

Wakilan Jam’iyyun sun fice ne bayan da shugaban hukumar zabe ta Ƙasa INEC Farfesa Mahmoud Yakubu ya magantu game da korafe-korafen da wakilan Jam’iyyun suka yi, kan yadda ake tattara sakamakon zaben.

Tun da farko dai wakilan Jam’iyyun sun nemi shugaban hukumar zaben ya ba da umarnin sanya gaba daya sakamakon mazabu a shafin intanet na hukumar kamar yadda aka tsara.

Sai dai shugaban na INEC ya bayyana musu cewa, za a duba korafe-korafen da jam’iyyu suka gabatar, amma kamar yadda yake bisa doka, za a yi hakan ne bayan tattara sakamakon zabe.

Ficewar ta su dai na alamta cewa ba su gamsu da bayanin da shugaban na INEC ya yi musu ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here