Shugaban ƙasa Bola Tinubu zai bar ƙasar Faransa a ranar Litinin zuwa birnin Cape Town, Afirka ta Kudu, don jagorantar zaman taron hadin gwiwa na 11 tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu (BNC) tare da Shugaba Cyril Ramaphosa.
Za a gudanar da taron a ranar 3 ga Disamba, yayin da za a fara zaman ministoci a ranar 2 ga Disamba a ginin Majalisar Dokokin Afirka ta Kudu da ke Cape Town.
A cewar Bayo Onanuga, mai ba shugaban ƙasa shawara kan bayanai da dabaru, Tinubu da Ramaphosa za su tattauna kan al’amuran hadin gwiwa na ƙasa, yankin Afirka, da na ƙasa da ƙasa.
Za su kuma duba ci gaban da aka samu tun bayan zaman taron BNC na 10 da aka gudanar a Abuja daga 29 ga Nuwamba zuwa 1 ga Disamba, 2021, tare da mayar da hankali kan yarjejeniyoyin da aka cimma a ganawar su ta ranar 20 ga Yuni a Johannesburg.
“Zaman taron BNC na 11 zai kunshi tattaunawa kan fannoni guda takwas, waɗanda suka haɗa da shawarar siyasa, al’amuran shiga da fita, banki da kuɗi, tsaro da kariya, masana’antu, bangaren zamantakewa, hakar ma’adinai da makamashi, da kuma kasuwanci da zuba jari,” in ji sanarwar.












































