Tinubu zai gana da kamfanonin samar da lantarki kan bashin tiriliyan huɗu – Minista

images 1 3 678x430

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai gana da shugabanni na kamfanonin da ke samar da lantarki a ƙasar domin tattaunawa kan bashin naira tiriliyan huɗu da suke bi.

Wata sanarwa da mai magana da yawun Ministan Lantarki Adebayo Adelabu ya fitar ranar Lahadi ta ce gwamnatin tarayya ta ƙagu ta shawo kan matsalar bayan ganawar da ministan ya yi da shugaban kamfanonin ranar Talata.

Yayin ganawar, ministan ya tabbatar wa kamfanonin da ake kira Generation Companies (GenCos) cewa gwamnati za ta mayar da hankali wajen wani ɓangare na bashin, in ji sanarwar.

Karin karatu: Daliban Al-Qur’ani 300 sun isa jihar Bauchi domin gudanar da Musabaƙar shekara

“Akwai buƙatar mu biya wani babban ɓangare na kuɗin hannu, idan ya so daga baya sai mu nemi a yi mana lamuni na biyan ragowar nan gaba,” a cewar ministan kamar yadda Bolaji Tunji ya ruwaito cikin sanarwar.

Ta ƙara da cewa za a daddale abin da gwamnatin za ta biya ne yayin ganawar tsakanin shugaban ƙasa da shugabannin kamfanonin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here