Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Olatunji Disu, ya kaddamar da kwamitin mutum takwas domin aiwatar da ‘yan sandan jiha.
Yayin kaddamar da kwamitin ranar Laraba a Abuja, Disu ya ce kwamitin na da wata guda domin mika rahotonsa.
Ya ce aikin da ke gaban kwamitin yana da muhimmanci kuma ya dace da lokacin da ake ciki, domin yana da nasaba da bukatar karfafa tsaron cikin gida na Najeriya.
Ya kara da cewa manufar ita ce a tabbatar da cewa aikin ‘yan sanda a Najeriya ya kasance mai dacewa da halin da ake ciki a kasa.
Ya ce kwamitin zai taimaka wajen tsara tsarin da ‘yan sandan jiha za su yi aiki a Najeriya ta hanyar da za ta karfafa tsarin tsaron kasa maimakon rarraba shi.
A cewarsa, kwamitin zai duba tsarin aikin ‘yan sanda da ake da su a ciki da wajen Najeriya tare da tantance bukatun tsaron al’umma da sabbin barazana.
Disu ya ce kwamitin zai gabatar da tsarin aiki kan kafawa da daidaita ‘yan sandan jiha tare da bayar da shawarwari kan daukar ma’aikata, ka’idojin horaswa da rarraba kayan aiki.
Ya ce za a samar da ingantattun hanyoyin sanya ido da tabbatar da gaskiya domin tabbatar da kwarewa da amincewar jama’a.
Ya bayyana cewa idan aka tsara da kyau kuma aka aiwatar yadda ya kamata, ‘yan sandan jiha na da damar kawo gagarumin anfani ga kasa.
Ya ce rarraba wasu ayyukan ‘yan sanda zai taimaka wajen inganta amfani da kayan tsaro, yayin da Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da mai da hankali kan manyan batutuwan tsaron kasa.
Sufeto Janar ya ce Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya za ta ci gaba da taka rawarta ta kundin tsarin mulki a matsayin babbar cibiyar tabbatar da doka da oda a cikin gida.
Ya kara da cewa ‘yan sandan tarayya za su fi mayar da hankali kan manyan laifuka masu sarkakiya da na ketare iyaka kamar ta’addanci, manyan kungiyoyin laifi, laifukan intanet da safarar mutane da ke bukatar hadin kai na kasa.
Ya tabbatar wa jami’ai da ma’aikatan Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya cewa muhimmancinsu da rawar da suke takawa a tsarin tsaron Najeriya na nan daram kuma ba za a iya musun su ba.
Ya bukaci kwamitin da su gudanar da aikinsu da jajircewa da kishin kasa, yana mai cewa sakamakon aikinsu zai taka muhimmiyar rawa wajen tsara makomar aikin ‘yan sanda a Najeriya.













































