Saudiya ta fitar da sababbin dokoki ga kamfanonin da za su yi jigilar mahajjatan bana

NAHCON NEW 1
NAHCON NEW 1

Hukumar kula da sifurin jiragen sama ta ƙsar SaudiArabiya, ta fitar da sababbin dokoki ga kamfanonin jiragen sama da za su yi jigilar alhazan bana.

Dokokin sun shafi duk jiragen da suke gudanar da  harkokin su a filin tashi da saukar  jirge na ƙasar da su tabbatar da mahajjatan da za su su kawo sun cika sharuɗan da aka basu dangane da sha’anin lafiyar su.

Sababbin dokokin sun haɗa da, mahajjatan bana dole ne su zama ƴan ƙasa da shekaru 65 da haihuwa, sannan kuma sai sun gama karɓar allurar rigakafin cutar Corona.

Haka kuma dole mahajjatan su gabatar da shaidar gwajin da ke nuna cewa ba sa ɗauke da cutar Corona, sananan  gwajin ya zamo an yi shi ne sa’a 72 kafin mahajjatan  su tashi zuwa kasar ta Saudiya.

Adadin kujerun da kamfanonin jiragen sama na ƙasashen waje da za su samar wa da alazan su sun kai  kimanin 107,000, Sannan kuma  jiragen da za su yi jigilar mahajjatan cikin ƙasar Saudiyar  suma za su samar da kujeru 12,800 a hajjin bana.

Wannan dai shi ne karon farko da mahajjatan ƙasashen waje za su  shiga ƙasar ta Saudiya don yin aikin hajji, tun bayan shekara biyu da ƙasar ta dakatar da ƴan kasashen waje daga yin aikin hajji sakamakon ɓarkewar cutar Corona a fadin  duniya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here