NLC ta umurci ƙungiyoyi da suke da alaƙa da ita da su fara shirin yajin aiki kan rukunin kamfanonin Dangote

NLC

Ƙungiyar Ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta bayar da umarni ga dukkan ƙungiyoyin da ke ƙarƙashinta da su fara gaggawar shirye-shiryen yajin aiki a kan rukunin kamfaninin Dangote.

Wannan umarni ya fito ne daga wata takarda wadda shugaban NLC, Mista Joe Ajaero, ya rattaba hannu a kai a ranar Litinin a Abuja.

Matakin ya biyo bayan rikicin da ya taso tsakanin kamfanin mai na Dangote da ƙungiyar manyan ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya (PENGASSAN) kan zargin korar ma’aikata sama da 800.

Ajaero ya ce an dauki matakin ne saboda abin da ƙungiyar ta bayyana a matsayin “yakın adawa da ma’aikata” da kamfanin Dangote ke yi.

Ya zargi kamfanin da saba wa sashe na 40 na kundin tsarin mulki da kuma yarjejeniyoyin ILO lamba 87 da 98, waɗanda ke kare ‘yancin ma’aikata na kafa ƙungiya da shiga ƙungiya.

Karin labari: Kotu ta hana PENGASSAN da wasu katse ayyukan kamfanin man Dangote

Ya bayyana cewa an umurci dukkan ƙungiyoyin da ke ƙarƙashin NLC da su kasance cikin shiri tare da fara ƙoƙarin shigar da ma’aikata cikin ƙungiya a dukkanin wuraren kamfanin Dangote da ke yankunansu.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) ya ruwaito cewa gwamantin tarayya ta kira wani taron sasanci domin hana rikicin Yayi ƙamari.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here