NAHCON ta jaddada kudirinta na yin shirye-shiryen aikin Hajjin 2026 cikin lokaci da tsari

NAHCON Chairman Prof Abdullahi Saleh Usman sabo 750x430

Shugaban Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya jaddada kudirin hukumar na yin shirye-shiryen aikin hajjin 2026 cikin lokaci da kuma bin tsari yadda ya dace domin tafiyar da aikin cikin nasara.

Sanarwar da mataimakinsa na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Ahmad Mu’azu, ya fitar ta bayyana cewa hukumar ta dukufa wajen inganta haɗin kai da bin ƙa’idojin da aka tanada domin gudanar da aikin hajji ba tare da tangarda ba.

Hukumar ta bayyana cewa tana aiki ne bisa manufofin gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, inda ajandar Sabunta Fata “Renewed Hope” ke bai wa walwalar mahajjatan Najeriya da jin daɗin addininsu muhimmanci.

NAHCON, wadda ke aiki a ƙarƙashin kulawar Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, ta bayyana cewa ta ba da fifiko ga kammala muhimman shirye-shiryen aikin hajji cikin lokaci, musamman shirye-shiryen masaukin mahajjata na jihohi a birnin Makkah bisa ƙa’idojin da Masarautar Saudiyya ta shimfiɗa.

A wani bangare na matakan tsari na ciki, shugaban NAHCON ya amince da tura wata babbar tawagar shugabanni zuwa Masarautar Saudiyya domin kula da manyan ayyuka, kammala dukkan shirye-shiryen masauki a Makkah da kuma tabbatar da bin ƙa’idojin Saudiyya domin kauce wa jinkiri ko matsala a aiki.

Tawagar ta ƙunshi kwamishinan tsare-tsare, bincike, kididdiga, yaɗa labarai da ayyukan ɗakunan karatu, Farfesa Abubakar Yagawal, da mamba na hukumar daga shiyyar Arewa maso Yamma, Sheikh Muhammad Bin Uthman, tare da wasu mambobin hukumar daga sauran shiyyoyi da kuma sakataren hukumar.

Hukumar ta kuma bayyana cewa an kunna dukkan hanyoyin sa ido, shugabanci da daidaito na cikin gida domin tabbatar da gaskiya, bin doka da kuma aiwatar da dukkan shirye-shiryen yadda ya dace, tare da tabbatar wa masu ruwa da tsaki da mahajjatan da ke shirin tafiya cewa NAHCON na da cikakken mayar da hankali wajen gudanar da aikin hajji cikin kwarewa da kwanciyar hankali, bisa ƙa’idojin ƙasa da na ƙasa da ƙasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here