Mutane da dama sun mutu sakamakon arangamar sojoji da ‘yan ta’adda a Plateau

'Yan bindiga, Kujuru, mata, sace, hari
‘Yan bindiga sun sake kai wani sabon hari garin Banono da ke karkashin masarautar Kufana ta karamar hukumar Kajuru da ke jihar Kaduna a tarayyar Najeriya,..

Rahotanni sun bayyana cewa an kashe mutane da dama yayin da sojoji da ‘yan bindiga suka yi arangama a wasu kauyuka biyu na karamar hukumar Mangu ta jihar Filato.

Rikicin ya faru ne bayan Gwamna Caleb Mutfwang ya sassauta dokar hana fita ta sa’o’i 24 da aka sanya a yankin.

Mutfwang ya ce bayan inganta tsaro, ya kamata a sanya dokar hana fita daga karfe 8 na safe zuwa 4 na yamma.

Karanta wannan:Yan Bindiga sun sake kai wani sabon hari Jihar Plateau

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa an kashe ‘yan bindiga kusan 30 yayin da wasu sojoji suka samu raunuka a rikicin da aka yi a kauyukan Satguru da Tyop.

Wani jami’in tsaro da ya bukaci a sakaya sunansa ya shaidawa jaridar Daily trust cewa, “Lamarin ya faru ne tsakanin karfe 7 zuwa 7:30 na safe, inda ‘yan bindigar suka zo da yawansu, suka fara kai farmaki kan wasu al’ummomi da ke kan hanyar Gindri.

Karanta wannan: AA Rano ya kaddamar da sabon dakin karbar magani a AKTH wanda Sanata Ibrahim Shekarau ya gida

Ba tare da bata lokaci ba, an sanar da sojojin kuma nan take suka kai dauki.

Wata majiya a yankin da ta nemi a sakaya sunanta ta tabbatarwa Daily trust faruwar lamarin, inda ta ce har yanzu mutane na cikin fargaba.

Kakakin rundunar ‘Operation Safe Haven’ da ke aiki da jami’an wanzar da zaman lafiya a yankin, har yanzu bai amsa tambayoyin manema Labarai ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here