Mutane 13 sun kone kurmus, daya ya jikkata a wani hatsarin mota a jihar Ondo- FRSC

Accident Accident

Hukumar kiyaye haddura ta tarayya, (FRSC) reshen jihar Ondo, ta ce akalla mutane 13 ne suka kone kurmus a hanyar Ikare-Akoko/ Owo ranar Asabar a jihar.

Samuel Ibitoye, kwamandan hukumar FRSC reshen jihar ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai ranar Asabar a Akure.

“Hukumar FRSC ta yi nadamar sanar da jama’a wani hadarin mota da ya afku a yau Dec.28, a Abule Panu gaban gadar Ose, kan babbar hanyar Owo-Ikare, jihar Ondo.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here