Ministan yada labarai ya jagoranci tawagar Najeriya zuwa taron ƙungiyar masu kafafen yada labarai da ke gudana a Amurka

Minister of Information and National Orientation Mohammed Idris 720x430

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Alhaji Mohammed Idris, ya jagoranci tawagar Najeriya zuwa taron kungiyar masu kafafen yada labarai ta kasa (NAB) don halartar taron karawa juna sani na shekarar 2025 a birnin Las Vegas na kasar Amurka.

Taron, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito, shine don karfafa haɗin gwiwar watsa shirye-shirye da kuma kulla kawance.

Taron NAB, ya fara gudana daga ranar Asabar zuwa Laraba, kuma an yi masa take da: “Fasaha, shuhura, nan gaba.”

NAN ta kuma ruwaito cewa taron zai mayar da hankali ne kan batutuwa da dama, da suka hada da sabuwar fasahar zamani ta AI, hangen nesa, tattalin arziki da dai sauransu.

Ministan kamar yadda NAN ta ruwaito yana tare da manyan jami’an hukumomi a ma’aikatar, da suka hada da Manajan Daraktan NAN, Ali Muhammad Ali, da Darakta Janar na Hukumar Talabijin ta Najeriya, Salihu Dembos.

Sauran sun hada da Darakta-Janar na Hukumar Yada Labarai ta Kasa, Charles Ebuebu da Darakta Janar na Hukumar Kula da Tallace-tallace ta Najeriya.

Haka kuma a cikin tawagar akwai Darakta-Janar na Muryar Najeriya, Jibrin Ndace.

NAN ta ba da rahoton cewa taron NAB yana jan hankalin dubban shugabannin masana’antu daga ko’ina cikin duniya.NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here