Masu buƙata ta musamman a jihar Kano sun jaddada kiran kafa hukumar kula da su domin biyan bukatunsu.
Jaridar SolaceBase ta ruwaito sun koka da cewa duk da irin tabbacin da gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar, kafin zaben da kuma bayan zaben, bukatar ba ta cimma ruwa ba, wanda hakan ya sanya masu buƙata ta musamman cikin takaici kan jinkirin da aka samu.
Bisa la’akari da haka, kungiyar agaji ta Volunteer Overseas (VSO), tare da hadin gwiwar kungiyoyin kare hakkin masu buƙata ta musamman a Kano, sun shirya taron tattaunawa don tsara dabarun tabbatar da ayyukan hukumar.
Da yake jawabi a wajen taron, shugaban sashen kula da masu buƙata ta musamman na VSO, Aftahana Dahiru Sarina, ya jaddada bukatar su ci gaba da yin kiraye-kiraye har sai gwamnati ta yi abin da ya kamata.
Karanta: Kano: Naira Biliyan 30 na kasafin kudin kula da yanayi ci gaba ne, amma ana bukatar kari – Dr. Kani
Shugaban kungiyar masu lalurar laka Abdul Danladi Haruna ya jaddada muhimmancin samar da hukumar, inda ya jaddada cewa ya kamata masu buƙata ta musamman su da kansu su jagoranci hukumar.
Daraktar jin dadin jama’a ta ma’aikatar mata da yara da masu buƙata ta musamman ta Kano, Binta Muhammad Yakasai ta tabbatar da cewa gwamnati na bakin kokarinta wajen ganin an kafa hukumar.
Taron ya kara da cewa, ”Idan aka kafa hukumar, ana sa ran hukumar za ta zama mai canza rayuwar masu buƙata ta musamman, tare da tabbatar da sun samu damammaki daidai-da-kowa a fannin ilimi, kiwon lafiya, aikin yi, da kayayyakin more rayuwa.