Sarkin Musulmi ya ayyana ranar Lahadi a matsayin sabuwar shekarar Musulunci

Sarkin, Musulmi, ayyana, ranar, Lahadi, sabuwar, shekarar, Musulunci
Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya ayyana ranar Lahadi 7 ga watan Yuli, 2024, a matsayin...

Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya ayyana ranar Lahadi 7 ga watan Yuli, 2024, a matsayin ranar 1 ga watan Muharram, wacce ta zama farkon sabuwar shekarar Musulunci ta 1446 bayan Hijira.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addini na majalisar Sarkin Musulmi, Sambo Junaidu, a ranar Juma’a.

Ya bayyana cewa babu wani rahoton ganin watan da kwamitocin ganin wata na kasa da kuma wasu suka yi a fadin kasar.

Karin labari: Gwamnatin Kano ta bayyana ranar Litinin a matsayin hutu

Sanarwar ta ce, “Kwamitocin ganin wata na kasa da wasu a fadin kasar nan ba su samu rahoton ganin jinjirin watan Al-Muharram ba a ranar Juma’a 5 ga watan Yuli, 2024 wato 29 ga watan Zulhijja shekara ta 1445 bayan hijira.

“Amma ranar Asabar 6 ga watan Yuli, ita ce 30 ga watan Zulhijja.”

Sarkin Musulmin ya taya musulman Najeriya murnar shiga sabuwar shekara, ya bukace su da su ci gaba da yiwa Najeriya addu’o’in zaman lafiya da ci gaba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here