An kama wasu da ake zargin barayin kayayyakin TCN ne a Kaduna

Hanyoyin, wuta, kama, zargin, barayin, kayayyakin, TCN, Kaduna
Hukumar TCN, ta ce rundunar ‘yan sanda a jihar Kaduna ta kama wasu mutane hudu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne da aka kama suna lalata tashoshin wuta...

Hukumar TCN, ta ce rundunar ‘yan sanda a jihar Kaduna ta kama wasu mutane hudu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne da aka kama suna lalata tashoshin wuta a wasu sassan jihar.

Misis Ndidi Mbah, Babban Manajan Hukumar TCN, da Hulda da Jama’a ne ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a Abuja ranar Juma’a.

Karin labari: Sarkin Musulmi ya ayyana ranar Lahadi a matsayin sabuwar shekarar Musulunci

Babban manajan ta ce an kama mutanen da wasu kayayyaki na ta’adi.

Mbah ta ce TCN ta yaba da kokarin ‘yan sanda tare da ba da tabbacin ci gaba da hada kai da jami’an tsaro wajen kare ababen more rayuwa a fadin kasar.

“Za a gurfanar da wadanda ake zargin nan ba da jimawa ba,” in ji ta. Kamar yadda NAN ta ta tabbatar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here