Ministan bunƙasa ma’adinai Dakta Dele Alake, ya bayyana cewa ya dace a rufe dukkan makarantu da ke Najeriya wadanda suke karɓar kuɗin karatu da kuɗin ƙasashen waje.
Ya bayyana haka ne a lokacin bikin ranar zinariya ta Najeriya, wanda aka gudanar a gefen taron makon ma’adinai na Najeriya karo na goma a birnin Abuja, mai taken “Ma’adinai a Najeriya: Daga ci gaba zuwa tasiri a duniya.”
Alake ya bayyana wannan dabi’a ta karɓar kuɗin waje a matsayin wata babbar hanya ta ɓarnar tattalin arziki da take janyo cikas ga bunƙasuwar ƙasar.
Ya ce yana shirin gabatar da shawara ga majalisar zartarwa ta tarayya domin a rufe dukkan irin waɗannan makarantu.
A cewarsa, iyaye da ke biyan kuɗin makaranta da dalar Amurka ko fam ɗin Birtaniya ga ‘ya’yansu da ke karatu a cikin Najeriya, suna tilasta neman kuɗin waje daga kasuwa, wanda hakan ke ƙara tsadar dalar Amurka da rage darajar naira.
Ya ce ba a iya buɗe makaranta a ƙasashen waje a karɓi kuɗin Najeriya, amma abin mamaki, a nan ne ake yin hakan.
Ministan ya jaddada cewa lokaci ya yi da ‘yan ƙasa su sauya tunani da dabi’a, su maida hankali kan abubuwan da za su inganta, su samar da abin amfani da ci gaban ƙasa.
Ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na ɗaukar matakai daban-daban ciki har da tsarin amfani da fasahar zamani don hana ɓarna da rufe duk wata kafa ta asarar kudaden shiga a harkar sarrafa zinariya ta ƙasa.
A cewar sa, shirin sayen zinariya na ƙasa, wanda ake aiwatarwa ta asusun bunƙasa ma’adinai masu daraja, yana taimakawa wajen ƙarfafa ajiyar kuɗin waje da kuma ƙarfafa darajar naira.
Shirin yana bai wa gwamnati damar sayen zinariya daga masu hakar ƙanana da kuɗin Najeriya maimakon kashe kuɗin waje wajen sayen zinariya daga ƙasashen waje.
A nata jawabin, daraktar gudanarwa ta asusun bunƙasa ma’adinai masu daraja, Hajiya Fatima Shinkafi, ta bayyana cewa harkar zuba jari a zinariya a Najeriya tana ƙaruwa, sabanin yadda yake a wasu ƙasashe.
Ta ce zinariya tana da muhimmanci wajen kare tattalin arziki, kuma ta ƙarfafa mahalarta taron su tallafa wa burin gwamnati na mayar da Najeriya cibiyar hakar ma’adinai a duniya.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa taron makon ma’adinai na Najeriya daga ranar 13 zuwa 15 ga Oktoba, ya samu haɗin gwiwar ƙungiyar masu hakar ma’adinai ta Najeriya, kamfanin bincike na PricewaterhouseCoopers da ƙungiyar VUKA Group.













































