A ranar Laraba mai zuwa ne majalisar wakilai ta 9 za ta yi wani zama da dukkan wakilai, gabanin kaddamar da majalisar wakilai ta 10 a ranar 13 ga watan Yuni.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da magatakardan majalisar wakilai Dr Yahaya Danzaria ya sanyawa hannu a ranar Talata.
Jaridar Solacebase ta ce yayin zaman, ana sa ran shugaban majalisar, Femi Gbajabiamila zai gabatar da jawabinsa yayin da manyan jami’an majalisar za su gabatar da sakonnin fatan alheri.
Haka kuma taron zai gabatar da sakonnin fatan alheri daga ‘yan majalisa, tsoffin shugabannin majalisar, tsofaffin magatakarda a majalisar dokokin kasar,” in ji sanarwar.
Ya ce yayin zaman majalisar za ta mika wa ‘yan majalisar takardar shaidar zama mamba ta majalisar.