Ɗan takarar mataimakin gwamna na jam’iyyar APC a zaben 2023, Murtala Sule Garo, ya taya tsohon karamin ministan gidaje da ci gaban birane, Abdullahi Tijjani Gwarzo, murnar zagayowar ranar haihuwarsa wadda ya cika shekaru 65.
A sakon taya murna da ya fitar a ranar Laraba, Murtala Garo, wanda shi ne Galadiman Garo, ya bayyana Gwarzo a matsayin jagora mai ƙwazo wajen hada kan al’umma tun daga tushe.
Ya ce tafiyarsa a harkokin mulki ta nuna hangen nesa da jajircewar sa ga ci gaban Najeriya.
Garo ya jaddada cewa rawar da Gwarzo ya taka a matsayinsa na ƙaramin ministan gidaje da ci gaban birane ta kasance abin koyi da darasi ga sabbin shugabanni.
Ya ce hidimar da ya bayar a matakai daban-daban ya zame wa jama’a abin alfahari da tunawa.
Murtala Garo ya kuma bayyana godiyarsa bisa jagoranci da shawarwari da Gwarzo ya rika bashi tsawon shekaru.
Ya yi masa fatan lafiya, kwanciyar hankali, ƙarin ƙarfi da sabbin damar ci gaba domin ci gaba da zame wa al’umma abin koyi.
Ya ƙare da addu’a ga Allah Madaukakin Sarki ya cika masa shekaru masu albarka tare da nasara, yana mai cewa: “Barka da zagayowar ranar haihuwa da cika shekaru 65 a duniya “.













































