Kwamitin majalisar wakilai kan yiwa kundin tsarin mulkin kasa kwaskwarima ya yi watsi da kudirin ƙirkiro jihohi 31 saboda gaza cika sharuddan tsarin mulkin kasa.
Majalisar dai ta karbi ƙudiri kan ƙirƙirar sabbin jihohi 31 a ranar 6 ga Fabrairun 2025.
Da yake jawabi a ranar Juma’a a wajen taron komawa ga mambobin kwamitin da aka gudanar a garin Uyo na jihar Akwa Ibom, Benjamin Kalu, mataimakin kakakin majalisar kuma shugaban kwamitin, ya ce yayin da shawarwarin ke nuna muradin yankuna daban-daban, babu wanda ya bi tanadin sashe na 8 na kundin tsarin mulkin kasa na shekarar 1999, wanda ya zayyana ka’idojin samar da jihohi, domin sashen da aka ambata a baya ya bayyana buƙatun tsarin mulki don ƙirƙirar ƙasa.
Da yake jawabi a wurin taron Kalu, mataimakin kakakin majalisar ya ce ya kamata a sake gabatar da shawarwarin tare da bincike ga kundin tsarin mulki kafin ranar 5 ga Maris.
Ya kara da cewa kwamitin na iya yin la’akari da kara tsawaita wa’adin, ya danganta da tattaunawar da aka yi, sai dai a halin yanzu kwamitin na duba wasu kudirori 151 na gyaran kundin tsarin mulkin kasar nan da suka hada da tsarin gwamnatin tarayya, raba madafun iko, cin gashin kan kananan hukumomi, rabon kudaden shiga, gyare-gyaren shari’a da zabe, tsaro, ‘yancin mata da kuma hakkin dan Adam.
Kalu ya kara da cewa, kwamitin ya shirya taron jin ra’ayoyin jama’a na shiyyoyi da na kasa baki daya a shiyyoyin siyasa guda shida kan kudirin gyaran kundin tsarin mulkin kasar nan.