Majalisar Dattawa Najeriya, ta hannun kwamitinta kan kasafi, ta sanya ranar 17 ga Maris, 2026 a matsayin ranar da za a kammala tattaunawa tare da amincewa da kudirin kasafin kuɗin shekarar 2026 da ya kai naira tiriliyan 58.472.
Wannan bayani ya fito ne bayan wani zama na musamman da majalisar ta gudanar, inda ta amince da ware ranakun 2 zuwa 13 ga Fabrairu, 2026 domin nazari da tantance kimar kasafin kuɗin a matakin kwamitoci daban-daban na majalisar.
Kwamitin ya kuma sanya ranar Litinin 9 ga Fabrairu, 2026 domin gudanar da sauraron ra’ayoyin jama’a kan kudirin kasafin kuɗin shekarar 2026, domin bai wa al’umma da masu ruwa da tsaki damar bayar da shawarwari.
Shugaban kwamitin kasafi na majalisar dattawa, Sanata Solomon Olamilekan Adeola, ya bayyana cewa an tsara ranar 5 ga Maris, 2026 domin zaman tattaunawa tsakanin mambobin kwamitin da manyan jami’an tattalin arzikin gwamnatn tarayya, ciki har da Ministan kuɗi kuma Ministan da ke da alhakin kula da tattalin arziki, Wale Edun, da Ministan kasafi da tsare-tsaren ƙasa, Atiku Bagudu.
Ya kuma bayyana cewa daga ranar 16 zuwa 23 ga Fabrairu, 2026, shugabannin kwamitocin dindindin na majalisar dattawa za su miƙa rahotannin kare kasafi, kafin a gabatar da rahoton kwamitin kasafi ga majalisar dattawa a ranar 17 ga Maris.
Sanata Adeola ya ƙara da cewa duk da shugabancin majalisar dattawa ya so a amince da kasafin kafin ranar 12 ga Maris, 2026, an ƙara mako guda domin bai wa ‘yan majalisa damar yin cikakken bincike da nazari kan dukkan sassan kasafin kuɗin.













































