Kasar China Ta Rufe Shafukan Labaran Karya Dubu 100.

A kokarin tsaftace ingantattun labarai, Kasar Sin na cigaba da jan damara wajen kawar da labaran karya da jita-jita a shafukan sada zumunta, inda ta rufe shafukan sada zumunta na labaran karya sama da 100,000 a cikin wata guda wadanda ke ba da labarin karya.

Hukumar kula da sararin samaniya ta kasar Sin ta sanar da cewa ta kaddamar da wani shiri na musamman na tsaftace bayanan yanar gizo, tare da mai da hankali kan shafukan sada zumunta da ke yada “labarai na karya” da kuma yin kwaikwayon kafofin yada labarai na gwamnati.

Hukumar ta ce ta kulle shafuka sama da Dubu 107 na rukunan dandalin sada zumuntar labarai na jabu guda 835,000 na bayanan karya tun ranar 6 ga Afrilu.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Sin da kasashen duniya ke fama da ta’annatin labaran karya a yanar gizo.

Gwamnatin kasar Sin ta dauki matakan gaggawa don goge su baki daya.

A ‘yan kwanakin nan, Hukumar ta lashi takobin murkushe munanan kalamai ta yanar gizo da ke dakushe martabar sahihan labarai da ‘yan kasuwa.

Idan za a iya tunawa a kwanan nan ne China ta kama wani mutum a gundumar Gansu bisa zargin sa da amfani da ChatGPT wajen samar da labarin karya game da hadarin jirgin kasa. (Reuters/NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here