Dan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar NNPP, Abba K Yusuf, ya yi rashin kakar sa, Hajia Aishatu Ahmad Sufi.
Jaridar Solacebase ta rawaitu cewa Hajia Mowa ta rasu ranar Juma’a a asibitin koyarwa na malam Aminu Kano AKTH, tana mai shekaru 103 a duniya.
Bayanin rasuwar ta ta na dauke cikin wata sanarwa da Bature Dawakin Tofa, wanda shine mai magana da yawun Abba K Yusuf, ya turowa Jaridar Solacebase yau Juma’a.
Sanarwar ta ce Hajia Aisha Sufi, ta mutu ta bar dan uwan ta Alkali Hussaini Sufi, tare da ‘ya ‘yan ta uku, wadan da suka hada da Malama Khadijatul-Najaatu, wacce ita ce mahaifiyar Abba Gida Gida.













































