Tsohon Gwamna Yahaya Bello ya ki amsa laifuka 16 da ake tuhumar sa

Yahaya Bello 2 750x430.jpeg

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, da wasu mutane biyu, sun ki amsa laifuka 16 da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa take zarginsu.

Tsohon Gwamna Bello, wanda shi ne wanda ake tuhuma na 1, ya musanta zargin da ake yi masa a gaban mai shari’a Maryann Anenih yayin da aka karanta musu.

Bayan sun amsa rokonsu, Lauyan wadanda ake kara, Joseph Daudu, ya gabatar da bukatar neman beli. Sai dai Lauyan EFCC, Kemi Pinheiro, ta ki amincewa da bukatar, tana mai cewa ya kare ne a watan Oktoba.
Da yake yin karin haske, Lauyan wanda ake kara ya ce bukatar da ta dace a gaban Kotun ita ce neman belin wanda ake kara na farko, wanda aka shigar a ranar 22 ga watan Nuwamba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here